fbpx
Sunday, June 26
Shadow

Hanya daya ce kawai jam’iyyar mu ta APC zata iya kayar da Atiku Abubakar, shine ta fito da dan takara daga Arewa>>Orji Kalu ya baiwa APC shawara

Sanata Orji Kalu ya bayyanawa jam’iyyar su ta APC cewa, hanya daya ce kawai zasu iya yin nasara akan Atiku Abubakar.

 

Yace shine su tsayar da dan takarar shugaban kasa daga Arewa.

 

Kalu ya bayyana cewa, wanda ya kamata a baiwa wannan takara a APC shine Sanata Ahmad Lawal, watau kakakin majalisar Dattijai.

 

Ya bayyana hakane jim kadan bayan da Atiku ya lashe zaben fidda gwani na jam’iyyar PDP.

 

Saidai ana tunanin Kalu na ta wannan hankoro ne dan ya samu mukamin mataimakin shugaban kasa.

Karanta wannan  Shugaba Muhammadu Buhari ya dawo Najeriya daga kasar Rwanda

 

Kalu dai ya fito takarar shugaban kasa amma a karshe kuma ya janyewa Sanata Ahmad Lawal.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.