Wednesday, July 24
Shadow

Hanyoyin kara kiba

Kara kiba musamman me tsabta ba wadda zata wuce kima ba na da kyau.

Saboda rama wadda ta wuce kima na iya zama matsala wadda zata sa ka rasa abubuwan kariya na jiki da zasu iya kaiwa ga raguwar karfin jiki ta yanda zaka rika karyewa cikin sauki.

Ga hanyoyin da za’a kara kiba cikin sauki:

A kara yawan abincin da ake ci, a rika cin abinci kadan-kadan a lokuta daban-daban a rana.

A rika shan madara, madara na taimakawa sosai wajan karin kiba me tsafta.

A rika cin kifi da kwai da wake.

A rika shan yegot, A ci chakulate a sha ice cream daidai gwarwado.

Rika motsa jiki.

Karanta Wannan  Danyen kwai yana kara kiba

A rika cin soyayyen dankalin Hausa dana Turawa da kwai.

A rika cin naman kaza.

A rika cin bindin rago, ko na sa.

A rika cin doya, Madarar Kwakwa.

Kar a sha ruwa kamin a ci abinci, saboda hakan zai sa a ji an koshi da wuri.

A rika zuna abinci a babban kwano.

A rika samun bacci me kyau.

Idan aka yi hakan lallai za’a samu kiba me lafiya.

Kada a sha sha ka fashe

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *