fbpx
Tuesday, August 9
Shadow

Har a jihohin da PDP ke mulki akwai ‘yan Bindiga dan haka kada ka kawo mana wani Uzuri kan gazawarka>>Sanata Shehu Sani ya mayarwa Gwamna Masari Martani

A dazune Muka kawo muku labarin yanda gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari ya zargi makiyan APC da daukar Nauyin ‘yan Bindiga dan bata mulkin jam’iyyar.

 

Yace masu son tsayawa takara a shekarar 2023 ne ke daukar nauyin ‘yan Bindigar.

Saidai a martaninsa, Sanata Shehu Sani ya wallafa a shafinshi na sada zumunta inda yace A kamar yanda ake kai hare-hare a jihohin APC, A jihohin da PDP ma ke mulki ana kai irin wadannan hare-haren dan haka kada gwamnan ya bada wani uzuri game da gazawarsa.

Sanata Sani ya bayyana hakane ta shafinshi na sada zumunta.

Leave a Reply

Your email address will not be published.