fbpx
Wednesday, August 10
Shadow

Har yanzu akwai alburushi a ciki na, cewar fasinja na jirgin kasa bayan ya samu ‘yanci daga hannun ‘yan bindiga

A jiya ranar talata muka ruwaito cewa ‘yan bindigar da suka kaiwa jirgin kasa na jihar Kaduna hari a ranar 28 ga watan Maris sun sake sako mutane biyar.

Inda a cikin mutanen wani Sidi Aminu Sharif ya bayyanawa manema labarai cewa har yanzu akwai alburushi a cikinsa da ‘yan bindigar suka harbe shi.

Inda yace sun kasa cire masa shi amma yanzu tunda ya samu ‘yanci zai yi kokari a cire masa don kar ya cutar da shi.

Mutanen guda biyar da suka samu ‘yancin a ofishin Malam Tukur Mamu suka sauka, wato Hadimin Sheik Ahmad Gumi.

Leave a Reply

Your email address will not be published.