Gwamnan jihar Neja, Sani Bello, ya ce ba a saki mutane 42 da barayi suka sace daga Kwalejin Kimiyya ta Gwamnati da ke Kagara a jihar ba.
Jita-jita ta yadu a ranar Lahadi cewa an saki daliban, sai a wani taro da manema labarai a Minna, Gwamnan ya karya ikirarin, ya kara da cewa har yanzu ana kokarin ceto su ba tare da samu wata matsala ba.