A jiyane aka samu Rahotannin dake cewa wai an sako fasinjojin jirgin kasan Kaduna zuwa Abuja da ‘yan Bindiga suka sace.
Saidai iyalan wadannan fasinjoji sun karyata wancan rahoto.
Hakanan kuma mawallafin jaridar Desert Herald shima ya musanta hakan inda yace a yi watsi da wannan magana ba gaskiya bace.
Yace ana dai kan tattaunawar yanda za’a sako mutanen kuma nan ba da jimawa ba in Allah ya yarda zasu kubuta.