fbpx
Thursday, February 25
Shadow

Har yanzu ban bar Jam’iyyar PDP ba – Femi Fani-Kayode

Tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, Femi Fani-Kayode, ya ce bai bar PDP zuwa APC ba.

Jawabin nasa na zuwa ne sa’o’i kadan bayan da gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya bayyana a wani taron manema labarai a yau a jihar Kogi, cewa Fani-Kayode, ya sauya sheka zuwa jam’iyya mai mulki ta APC.

Sanarwar tasa na zuwa ne kwanaki biyu bayan FFK ya gana da shi da sauran shugabannin jam’iyyar APC.

Da yake bayyana matsayin nasa ta shafinsa na Twitter, tsohon Ministan ya wallafa a shafinsa na Twitter;

Yace duk cewa na gana da jiga-jigan jam’iyyar APC kuma a yanzu muna cikin lokacin siyasa, ina nan a PDP daram dam.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *