Rahotanni sun bayyana cewa, har yanzu babban bankin Najariya, CBN bai sakarwa bankuna tsaffin kudade ba dan rabawa ‘yan Najariya.
Hakan na zuwane bayan da CBN din ya baiwa bankuna umarnin su fara baiwa jama’ar gari tsaffin kudade musamman na 500 da 1000.
Da yawa da suka je bankuna dan cire kudi sun ce basu ji dadi ba saboda yanda suka kasa cire kudin da suke so.
Wasu da suka zanta da Daily trust sun bayyana cewa bankunan sun rika basu tsakanin 5000 zuwa 20,000 ne.
Wani abin karin ciwon kai shine wasu masu sana’o’i basa son karbar tsaffin kudaden.