Hukumar ‘yansandan jihar Kano ta bayyana cewa, har yanzu dokar hana hawan Achaba na nan daram a jihar.
Kakakin ‘yansandan jihar, SP Abdullahi Haruna-Kiyawa ne ya tabbatar da hakan ga manema labarai a jiya, Juma’a.
Yace duk wanda aka kama ya karya wannan dokar za’a hukuntashi, inda yayi kira ga mutanen jihar su zama masu bin doka.