fbpx
Monday, August 15
Shadow

Har yanzu fa DSS sun hanani in canja kaya>>Nnamdi Kanu

Har yanzu hukumar ‘yansandan farin kaya ta DSS ta hana shugaban haramtacciyar kungiyar IPOB dake son kafa kasar Biafra, Nnamdi Kanu ya canja kayansa.

 

Lauyan Kanu, Ifeanyi Ejiofor ya bayyana cewa DSS sun ki bada hadin kai duk da kokarin iyalan Nnamdi Kanu na a canja masa kaya.

 

Ya bayyana hakane ranar Alhamis bayan gawar da yayi da Nnamdi Kanun a ofishin DSS.

 

Lauyan yace hakan kuma sabawa dokar da kotu ta bayar ne, inda yace hakanan DSS din ta ki bada hadin kai a samarwa Kanu magani saboda yana fama da rashin lafiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published.