Tsohon Mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana cewa har yanzu yana da karfi a jikinsa.
Atiku yace kuma akwai alamu masu karfi dake nuna cewa shine zai lashe zaben shugaban kasa a shekarar 2023.
Atiku ya bayyana hakane a yayin ganawa da wakilan jam’iyyar PDP na yankin kudu maso yamma.
Atiku yace yana da damar lashe zaben ganin irin kuri’un dabya samu a shekarar 2019 da suka kai miliyan 12.