fbpx
Wednesday, August 10
Shadow

Har yanzu Sancho yana so ya koma Premier lig amma Dortmund basu da ra’ayin rage farashin sama da euros miliyan 100 akan dan wasan

Borussia Dortmund baza suyi wa wata kungiya rangwame ba wajen siyar da tauraron dan wasan su Jadon Sancho yayin da suke burin karbar euros miliyan 110 a hannun kungiyar data shirya siyan dan wasan.

Sancho har yanzu yana so ya koma daya daga manyan kungiyoyin premier lig kuma ba shi da ra’ayin bukatar sabon kwantiraki a kungiyar Dortmund yayin da kwantirakin shi zai kare nan da 2022.
Kungiyar Manchester United da Chelsea suna cikin kungiyoyin dake harin siyan Sancho amma  da dukkan alamu sai an samun saukin cutar Covid-19 zasu siye shi.
Duk da cewa Sancho yana fama da rauni a wannan kakar wasan kuma hakan yasa daga benci yake fara buga wasanni, yayi nasarar jefa kwallaye har guda 14 kuma ya taimaka wurin cin kwallaye guda 16 a wasanni 21 daya buga.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.