fbpx
Monday, August 15
Shadow

Haramtacciyar kungiyar Biafra ta gargadi ‘yan siyasar kudu masu gabashin kasar nan dake babban birnin tarayya cewa kar su sake su dawo gida ba tare da Nnamdi Kanu ba

Haramtacciyar kungiyar Biafra ta gargadi shuwagabanninta da kuma ‘yan siyasar dake babban birinin tarayya Abuja cewa kar sake su dawo gida ba tare da Nnamdi Kanu ba.

A ranar 27 ga watan Yuni na shekarar 2021 gwamnati ta kamo shugaban haramtacciyar kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu daga kasar Kenya ta kulle shi inda take zarginsa da aikata ta’addanci.

Amma a kwanakin baya masu kare hakkin bil’adama na majalissar dinkin duniya sun kalubalanci gwamnatin Kenya da kuma Najeriya kan kama Nnamdi Kanu da suka yi.

Karanta wannan  Labari me dadi: 'Yan bindiga sun sako mutane 35 da sukayi garkuwa dasu a Millennium City dake jihar Kaduna

Wanda yanzu ma shugaban kungiyar ta Biafra, Emma Powerful ya gargadi shwagabannin kudu masu gabshin kasar dake zaune a babban birnin tarayya cewa kar su sake su dawk gida ba tare da shugabansu Kanu ba.

Domin yace ‘yan ta’addan dakw kaiwa babban birnin tarayya hari so suke suga bayan Nnamdi Kanu.

 

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.