fbpx
Sunday, August 7
Shadow

Haramtacciyar kungiyar IPOB ta bayyana dalilin dayasa gwamnatin tarayya taki bayar da belin shugabanta Nnamdi Kanu

Ifeanyi Ejiofor dan haramtacciyar kungiyar IPOB ya bayyana dalilin dayasa gwamnatin tarayya taki bayar da belin shugabansu, Nnamdi Kanu.

Inda yace gwamnatin taki bayar da belin ne domin tana so ya cigaba da zama a hannun hukumar DSS a garkame.

Kuma haka zata cigaba da daga shari’ar tasa domin bata son ya koma gida, wannan dalilin ne ma yasa har yanzu bata saurari asalin shari’ar tasa ba.

A karshe yace sau bakwai gwamnatin tarayya na daga shari’ar Nnamdi Kanu tun shekarar 2015 saboda bata son ta sake tafi so ya dawwama a garkame.

Leave a Reply

Your email address will not be published.