fbpx
Friday, August 12
Shadow

Haramtcciyar kuniyar IPOB ta gargadi babbar kwamishinar Birtaniya ta fasa ziyartar Kudu maso gabashin Najeriya idan bata shirya mutuwa ba

Haramatacciyar kungiyar IPOB ta gargadi babbar kwamishinar Birtaniya, Catriona Liang cewa fa fasa kawo masu ziyara yankin nasu idan har bata shirya mutuwa ba.

A jiya ranar alhamis ne mai magana da yawun kungiyar, Emma Powerful ya bayyana hakan, inda yace akwai miyagun mutanen da suka shirya kasheta idan ta kawo masu ziyarar.

Ya kara da cewa wannan shawara ce a gareta duk da cewa sun tsani ‘yan Biafra amma gara tayi zamanta a Birtaniya akan tazo a kasheta a Najeriya.

Domin yace an shirya ‘yan ta’addan su kai mata hari su kasheta a dora laifin akan ‘yan Biafra.

Leave a Reply

Your email address will not be published.