Saturday, July 13
Shadow

Harin Amurka da Birtaniya ya kashe mutum 14 cikin dare a Yemen

Gidan talabijin na Yemen da ke ƙarƙashin jagorancin ƴan Houthi ya ruwaito cewa an kashe mutum 14 ckin dare, yayin da aka jikkata mutum sama da 30 a lokacin wani hari ta sama da dakarun hadin gwiwa na Amurka da Birtaniya suka ƙaddamar.

Cibiyar da ke bai wa dakarun Amurka umurni ta tabbatar da kai harin wanda ta ce na ramuwar gayya ne kan mayaƙan Houthi da ke kai hare-hare a kan jiragen ruwa masu sufuri ta tekun Bahar-maliya, lamarin da ke haifar da tsaiko wajen shigi da ficen kaya a duniya.

Cibiyar ta ce makaman da ta harba sun faɗa kan inda suka ƙuduri kai harin guda 13, yayin da aka daƙile harin jiragensu marasa matuƙa takwas.

Karanta Wannan  Zamu rama kashe mana sojoji 5 da kungiyar IPOB suka yi, zamu tabbatar mun yi maganinsu>>Inji Hukumar sojojin Najeriya

A ƴan watannin nan mayaƙan Houthi na kai hare-hare cikin tekun Bahar-maliya, tekun da ake amfani da shi wajen jigilar kaya a fadin duniya, harin da suka ce na nuna goyon baya ne ga Falasdinawa a Gaza.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *