fbpx
Thursday, August 11
Shadow

Harin Boko Haram na Garin Auno: Shuwagabannin kasashen Duniya da suka yanke ziyarar da suke a wasu kasashe suka koma kasarsu bayan da wani mummunan Al’amari ya shafi jama’arsu

Tun bayan harin garin Auno da Boko Haram suka kai a jihar Borno da rahotanni suka bayyana cewa yayi sanadiyyar kashe mutane 30 a yayin da shugaban kasa, Muhammadu Buhari ke ziyara a kasar Ethiopia wajan taro kungiyar hadin kan Africa ta AU wasu ‘yan Najeriya nadabra’ayin shugaban ya yanke wannan ziyara tashi da yake ya dawo gida.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Wannan dalili yasa shafin hutudole.con yayi nazari akan yanda a bayan wasu shugawagabannin kasashen Duniya suka yanke ziyarar aiki da suke a wasu kasashen da ba nasu ba, suka koma gida saboda wani ibtila’in daya fadawa jama’arsu.

Na kwanakwannan shine wanda shugaban kasar Nijar, Mahamadou Issoufou ya yanke ziyarar aikin da yake a kasar Misra/Egypt ya koma gida nan take bayan da ‘yan ta’adda suka kaiwa sojojin kasar Hari inda suka kashe sama da guda 70.

A dai wannan taron daya gudana a Kasar Egypt wanda ya shafi harkar tsaron Africa, shugaban kasar Africa ta kudu, Cyril Rahamaphosa shima ya yanke ziyarar da yake a Egypt wajan taron inda ya koma sarsa saboda matsalar wutar lantarki da aka samu wanda yasa kasa ta fada cikin duhu na kuaan kwanaki 8.

A jiya shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya yanke yakin neman zaben da yake inda ya nufi wajan iyalan wasu sojoji 2 na kasar da aka kashe a kasar Afganistan dan jajanta musu.

Karanta wannan  Shugaba Ghana yace bai cewa Tinubu yaje ya nemi lafiya kuma ya janyewa Peter Obi ba

A watan Maris na shekarar 2019 data gabata, shugaban kasar Israil, Benjamin Netanyahu ya yanke ziyarar kwana biyu da yake a kasar Amurka inda ya koma gida da gaggawa saboda fargabar harin da Palasdinawa kan iya kaiwa kasar tashi.

Shugaban kasar Sudan ta kudu, Salva Kiir a shekarar 2012 ya yanke ziyarar da yake a kasar China saboda fargabar cewa kasar Sudan zata iya kaiwa kasarsa Hari.

A watan Yuni na shekarar 2019 data gabata, shugaban kasar Mali, Ibrahim Boubacar Keita ya yanke ziyarar da yake a kasar Switzerland ya koma kasarsa bayan harin kabilanci da ya yayi sanadiyyar kashe mutane 35.

Shugaba Buhari ya nuna Alhini kan harin Auno ta hanyar yin shiru na minti 1 a yayin gabawar da yayi da ‘yan Najeriya mazauna kasar Ethiopia.

A yau, Larabane shugaba Buhari ke cika kwanaki 5 cif kamar yanda aka tsara tun farko cewa zai yi a kasar ta Ethiopia inda zai dawo Najeriya a tau din.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.