An lalata sansanin ‘yan bindiga da ke kusa da kauyen Kambari a karamar hukumar Karim Lamido a jihar Taraba a wani harin da sojojin saman Najeriya suka kai ta sama.
Daily Trust ta tattaro cewa harin na sama wanda aka fara kwanaki uku da suka gabata, an kai shi ne a sansanonin ‘yan bindiga, inda aka ce an kashe ‘yan bindiga da dama.
Wakilin Daily trust ya samu labarin cewa an kashe wasu mutane 3 da ke kan babura a kewayen Kwatan Nanido da ke karamar hukumar Gassol a harin da jirgin ya kai.
A kokarin jin ta bakin kakakin rundunar sojin saman Najeriya abin ya ci tura.
Sai dai Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Taraba, DSP Usman Abdullahi, ya ce rundunar ta san da harin, inda ya ce rundunar sojin sama ce ta kai hare-haren.