Sajan Haruna Muhammad Funtua wanda yana daya daga cikin wadanda harin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna ya rutsa da su ya rasu.
Marigayin ya samu raunukan bindiga a kai da kirjinsa yayin harin kuma ya mutu a ranar Talata, 5 ga Afrilu.
A cewar Idris, wani dan jarida kuma malami, marigayi Haruna yana daga cikin dattawan al’ummarsa, karamar hukumar Funtua ta jihar Katsina, wadanda ke tallafa wa ’yan banga da sauran masu aikin sa kai na tsaro.
An kashe mutane 8 tare da jikkata wasu 26 a harin na ranar Litinin, 28 ga Maris
Allah ya jikansa da rahama ya kuma baiwa iyalansa hakurin jure wannan Rashi Amin.
