Yan bindigar da sukayi garkuwa dake rime da mutane 61 a harin da suka kaiwa jirgin kasa na Kaduna sun sako mutane 11 a cikin su.
Amma har yanzu dai ba’a samu cikakken rahoto akan yadda aka sako su ba sai dai an tafi dasu babban birnin tarayya jihar Abuja.
Mutanen sun hada da mata shida sai kuma maza guda biyar.
Harin jirgin kasan ya faru ne a ranar 28 ga watan maris wanda yayi sanadiyyar rayukan mutane 8 kuma wasu mutanen suka bace yayin akayi garkuwa da wasu, sannan mutane 26 suka samu raunika.