fbpx
Monday, August 15
Shadow

Harin Kuje: Majalissar Dattawa ta bayyana cewa jami’an tsaron Najeriya sun gaza tunda suka kasa kare harin da aka kaiwa gidan yarin Abuja

Majalissr Dattawa tayi Allah Wadai da harin da ‘yan ta’addan ISWAP suka kai gidan yari na Kuje dake babban birinin tarayya abuja a wannan makon.

Inda suka bayyana cewa jami’an tsaron kasa Najeriya sun gaza tunda suka kasa dakatar dasu alhalin sun dauki awanni suna aikata wannan bannar, kuma hae suka bude masu laifi suja tsere.

Shugaban sanatoci, Ahmad Lawal ne ya bayyana bayan ya ziyarci gidan yarin kuma ya bayyana bacin ransa sosai akan wannan mummunan harin.

Lawal yace ba zasu laminci wannan cin zarafin ba kuma yana kira ga shugaban gidan yarin ya bukaci a saka kyarori a gidan yarjn a kasafin kudin shekarar 2023.

Leave a Reply

Your email address will not be published.