fbpx
Friday, July 1
Shadow

Harin Texas: Ɗan bindiga ya harbe mutum 21 a Amurka

Wani dan bindiga ya kai hari a makarantar Firamare ta Robb Elementary da ke Texas a Amurka, inda ya kashe dalibai 19 da malamai biyu.

To amma jami’an tsaro sun yi nasarar bindige maharin mai suna Salvador Ramos mai shekaru 18.

Rahotanni sun ce matashin ya sayi manyan bindigogi masu sarrafa kansu guda biyu, ya kuma fara kashe kakarsa kafin ya isa makarantar.

Shine hari mafi muni da aka taba kaiwa makarantar Firamare a Amurka, tun bayan na shekarar 2012 da aka kai a Connecticut, inda aka kashe kananan yara 20 da malamai shida.

A jawabinsa a Fadar White House jim kadan bayan harin, Shugaba Joe Biden ya ce tabbas lokaci ya yi da zasu yi fito na fito da masu rajin mallakar bindiga a Amurka.

Mr Biden na jawabin ne cikin fushi, inda ya kara yana cewa ”don mi za mu yadda mu cigaba da zama cikin wannan kashe-kashe? Don me za mu bari haka ta cigaba da faruwa? Yanzu kam dole mu dauki mataki yanzu.”

Shugaban ya kara da cewa hankali ba zai dauka ba ace matashi dan shekara 18 zai iya shiga shago kai tsaye ya siyo manyan bindigogi hankalinsa kwance.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.