fbpx
Thursday, July 7
Shadow

Harry Kane ya zamo dan wasa na uku daya ci kwallaye 15 a wannan kakar yayin da Tottenham ta raba maki da Crystal Palace bayan sun tashi wasa 1-1

Harry Kane ya taimakawa Tottenham ta fara jagorancin wasanta da Crystal Palace a minti na 22, amma tawagar Jose Mourinho sun kasa kara jagorancin nasu a wasan, yayin da shi kuma Schlupp ya ramawa Palace kwallon a minti na 81 wadda  tasa suka raba maki.

Kwallon da Harry Kane yaci ta kasance kwallon shi ta tara a gasar Premier League na wannan kakar yayin da kuma kuma, kwallon tasa ya zamo dan wasa na uku daya ci kwallaye 15 a wannan kakar bayan Haaland yaci 17, sai Lewandowski wanda shi kuma yaci 16.
Ta bangaren gasar Serie A kungiyar Atalanta tayi nasarar lallasa Fiorentina 3-0 yayin da Bologna tasha kashi 5-1 a hannun Atalanta sai Inter Milan ta lallasa Cagliari 3-1 sai itama Napoli taci Sampdoria 2-1.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Karanta wannan  Shalelen PSG, Mbappe ya samu sabani da Messi kan sayar da Neymar a wannan kakar

Leave a Reply

Your email address will not be published.