fbpx
Thursday, June 30
Shadow

HASASHE: Mai yuwuwa Osinbajo ya kauracewa zuwa Sokoto ganawa da delegate saboda bacin ran ki$an Debor@h

Daga Muryoyi

Masu hasashen siyasa na ganin idan banda ya zama dole da mataimakin shugaban kasa Farfesa Pastor Yemi Osinbajo ya kauracewa zuwa jihar Sokoto neman kuri’un wakilan jamiyya wato deligate saboda tsananin bacin rai game da jifan shedan da ake zargin anyiwa wata daliba a Sokoto da tayi batanci ga Ann@bi S.A.W.

Masu hasashen na ganin sai dai kawai Osinbajo ba zai so ya rasa kuri’ar deligate din ba musamman ganin yadda masu neman takara a APC ke dada samun karbuwa wanda hakan babban kalubale ne a gareshi.

Tun bayan faruwar abun dai Osinbajo ya yi Allah-wadai da ki$@n dalibar inda yace kamar yadda shugaban kasa ya fadi ne komi munin tsokana babu wanda ya cancanci irin wannan mummunan kisa da akayiwa Debor@h Samuel

Karanta wannan  Rikici ya kunno kai a PDP saboda Atiku ya ki yadda da Wike a matsayin mataimakinsa

Ya ce abin takaici ne matuka yana mai nuna matukar bacin ransa akai

Muryoyi ta ruwaito Osinbajo wanda ransa ya matukar baci yace babu abunda ya sosa masa rai sai irin yanayin faruwar lamari yanayi mai ban tsoro da yarinyar ta mutu

A karshe mataimakin shugaban kasar ya jajantawa iyaye da yan’uwa da abokan dalibar bisa wannan abu da yace yasan yayi tsananin sosa masu rai sannan ya nemi a gaggauta kamowa a hukunta masu hannu a ciki.

Sai dai ana ganin ya zamar masa dole yaje Sokoto ko da ransa bai so ba muddin yana son kuri’un deligate din.

Me zaku ce?

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.