fbpx
Wednesday, August 10
Shadow

Haske yazo jihar Osun, cewar Atiku bayan Adeleke ya lashe zaben gwamnan jihar

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya taya Ademola Adeleke murna bayan ya lashe zaben gwamnan jihar Osun.

Inda yace haske yazo jihar ta Osun kuma yana mika sakon godiya ga daukacin al’ummar jihar da suka taimakawa jam’iyyar PDP tayi nasara.

Inda ya kara da cewa yana godiya ga masu hannu da tsaki a jam’iyyar tasu da suka fafata don ganin cewa PDP ta lashe zaben gwamnan jihar Osun.

PDP ta kwace mulkin ne a hannun gwamna Oyetola dan takarar APC wanda ya kayar da Adeleke a shekarar 2018.

Leave a Reply

Your email address will not be published.