fbpx
Saturday, September 19
Shadow

Hatsarin mota yayi sanadin mutuwar mutane shida a Ondo

Kimanin mutane shida ne aka tabbatar da mutuwarsu a wani hatsarin mota wanda ya afku a kan hanyar Akure  a karamar hukumar Ifedore ta jihar Ondo da yammacin Laraba.

A cewar wani ganau, wanda ya bayyana cewa hatsarin ya afku ne sakamakon rashin lura ga masu tukin motocin Wanda ta Kai ga faruwar lamarin.

Da take tabbatar da faruwar lamarin, mai magana da yawun rundunar reshen jihar Ondo na Hukumar Kiyaye Haddura (FRSC) Misis Tola Ogunbanwo, ta ce hatsarin ya faru ne sakamakon rashin maida hankali daga daya daga cikin direbobin motocin da lamarin ya rutsa da su.

A cewarta tuni an aike da mutane 7 da su ka samu mummunan rauni zuwa Asbiti, inda kuma a ka kai gawarwakin wadanda su ka mutu zuwa wajan ajiyar gawa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=hdlabarai.aplibwxLeave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *