Hukumar tana fasa kwauri ta kasa, Kwastam ta kama shinkafa me guba da aka shigo da ita cikin Najeriya.
Yawan shinkafar da aka kama ta kai tirela 12, an kuma kamata ne a watan Afrilun da ya gabata.
Sannan kuma an kama mutane 12 dake da hannu wajan shigo da shinkafar wadda ‘yar kasar wajece.
Jami’in hukumar, Hussein Ejebunu ya tabbatar da kamen.