fbpx
Thursday, February 9
Shadow

Hattara: Ji yanda tsaka ta yi sanadin mutuwar mutane 6 ‘yan gida daya

Mutane 6 ‘yan gida daya sun mutu bayan da suka ci wani gurbataccen abinci.

 

An bayyana cewa, tsaka ta hau kan abincin kamin suka ci suka mutu.

 

Lamarin ya farune da iyalan Adeleke John Samuel, da matarsa, da ‘ya’yansa biyu da wasu danginsu biyu.

 

Me gadinsu, Mr Lawal Ojo ne ya jawo hankalin mutane bayan da ya ji gidan shiru ba yanda ya Saba ji ba.

 

Shafin The Eagle ya ruwaito cewa da makwabta suka shiga gidan, sun tarar da mutanen a kwance basu tashi daga barci ba, ba rai.

 

Da aka bincika an ga gawar tsaka a cikin tukunyar miyarsu.

 

Saidai ‘yansanda har yanzu suna bincike dan tabbatar da dalilin mutuwar iyalan a hukumance.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *