Hedikwatar tsaron Najeriya za ta yi bincike kan ‘bidiyon ƴan bindiga a Katsina’
Hedikwatar tsaron Najeirya ta ce ta kaddamar da bincike kan wani bidiyo da ya yadu a shafukan sada zumunta da ke nuna wasu da ake zargin sojoji ne suna magana da wasu mutane a kan babura ɗauke da makamai, waɗanda ake tunanin ƴan fashin daji ne.
Ana zargin cewa, an ɗauki bidiyon ne a jihar Katsina da ke arewa maso yammacin Najeriya.
A cikin bidiyon an ji wani da ba a san ko wane ne ba, na bayyana cewa “an yi sulhu da mutanen kuma za a bar su, su wuce ba tare da an taɓa su ba.”
Wata sanarwa da mai magana da yawun hedikwatar tsaron ta Najeriya, Birgediya Janar Tukur Gusau ya fitar, hedikwatar ta ce maƙasudin gudanar da binciken shi ne a tabbatar da sahihancin bidiyon da kuma gano sojojin.
Sanarwar ta ƙara da cewa cibiyar na sane da cewa wasu ‘yan bindigan sun yanke shawarar tuba, kuma suna maraba da su.
Katsina na cikin jihohin da matsalar ƴan fashin daji ta yi wa katutu.
Ƴan bindigar kan sace mutane tare da garkuwa da su domin neman kuɗin fansa, haka kuma sukan tarwatsa ƙauyuka da satar kayan masarufi da dabbobi.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake ganin sojoji suna ƙokarin murƙushe masu aikata laifuka a yankuna daban-daban na ƙasar