fbpx
Monday, August 15
Shadow

Hidikwatar sojin Najeriya tace an kashe ‘yan bindiga 30 da suka kashe sojan dake tsaron shugaban kasa Muhammadu Buhari

Hudikwatar sojin Najeriya ta bayyana cewa rundunarta dake babban birnin tarayya ta 7 Guard dake tsaron shugaba  kasa ta dauki fansa kan aika aikar da ‘yan bindiga suka yi mata.

‘Yan bindigar sun kashe masu daya daga cikin shugabansu ne a Bwari bayan ya amsa kira da makarantar lauyoyi tayi masu biyo bayan wasikar da ‘yan bindiga suka aikawa makarantar cewa zasu kai mata hari.

Inda hedikwatar tace tsakanin ranar lahadi zuwa talata sun kashe ‘yan bindiga 30 kuma lalata masu mazauninsu.

Karanta wannan  Matsalar tsaro ta kare a Edo, domin gwamnati ta saka kyamarori a fadin jihar-kwamishinan 'yan sanda

Yayin da kuma suka kwato babura shida a hannunsu tare da manyan makaman da suka ta’addanci dasu.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.