Friday, July 12
Shadow

Hirar soyayya masu dadi

Ga wasu hirar masoya masu dadi kamar haka:

Babe ya kake.

Babyna sai a Hankali.

Me ya faru da kai?

Rashin jin miryarki ne ya sakani damuwa.

Har kasa gabana ya fadi, na sha wani abune ya sameka.

Au wannan ba wani abu bane?

Hmmmm….

Ai rashin jin muryarki babban abune a wajena.

Koh?

Eh mana, ko abinci na kasa ci, yanzu dai kimin voice note me dadi.

To shikenan, da muryar dawisu kake so in maka ko da muryar zakara?

Hahahahaha…. kin ban dariya, dama kin iya muryar zakara?

Au baka sani ba? Kaidai kawai ka zaba da wace kalar murya kake son jin muryata.

Karanta Wannan  Kalaman soyayya masu dadi

Ina son jin muryarki da asalin muryarki wadda na saba ji dan ta fi min kowacce dadi.

Hmmmm kasa naji dadi a zuciyata.

Ga wata Hirar soyayya me dadi:

Babyna, gani a kwance addu’a kawai ta rage in yi bacci nace bari in maka chattin mu yi magana.

Hmmm nima gani a kwance amma ni ko baccin ma bana ji tunaninki kawai nake.

Allah ko?

Eh mana!

To ai gani muna magana.

Hmmmmm ba zaki gane bane, tabbas ina jin dadin maganar da muke amma ina son mu kai mataki na gaba.

Ban gane mataki na gababa ba.

Eh mana, ya zamana muna bacci tare mu tashi tare mu ci abinci tare mu yi wasa da sauransu.

Karanta Wannan  Sunayen mata masu dadi

Hmmmm babe karka damu, me kake ci na baka na zuba? Ai indai da rai da lafiya in Allah ya yarda kamar hakan ta faru ta kare.

Wayyo Allah na, kin ji yanda zuciyata ta narke kuwa?

Hmm ai ina gaya maka akwai tanade-tanade dana mana ni da kai amma dai kawai sai lokaci yayi.

Dan gayamin mana wasu daga cikin tanadin da kika mana.

A’a gaskiya ba zan gaya maka ba, ina so ne kawai saidai ka gani.

Hmmmm da ina kwance har kinsa na tashi zaune, princess dina ai insha Allah dole in yi kokari in ga kin zama tawa inga yanda kalar rayuwar auren mu zata kasance.

Karanta Wannan  Soyayya text message

Kaidai bari insha Allahu zamu samu ‘ya’ya masu Albarka kuma muyi rayuwa har tsufan mu muna soyayya.

Amin babyna.

Naga dare yayi, duk ni ban gaji da hira dake ba amma nasan kina son ki kwanta, kar in shiga hakkinki, ki je ki kwanta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *