An yi kamenne a karamar hukumar Sule Tankarkar dake jihar.
Kakakin HISBAH na jihar, Muhammad Sale Korau ne ya tabbatar da hakan.
Yace sun kama maza 5 mata 5. Yace sun kuma yi nasarar kama kwalaben giya. Yace sun mika wanda ake zargin ga hannun jami’an tsaro dan daukar matakin da ya dace.
Ya jadada aniyar hukukarsu ta yaki da rashin da’a a cikin jiharsu.