fbpx
Sunday, May 22
Shadow

Hoto gwanin Ban tausai yanda magidanci ya zubawa tsohuwar matarsa fetur ya cinna mata wuta a jihar Adamawa

Wani magidanci a jihar Adamawa me suna Kuryanga ya bankawa tsohuwar matarsa wuta bayan ya zuba mata fetur.

 

Shekarar su 7 da aure amma kotu ta raba auren sannan ta saka mai iyaka da ita saboda yanda yake yawan cin zarafin tsohuwar matar tasa me suna Janet John.

 

Saidai duk da haka bai kyaleta ba.

 

‘Yar uwar matar, Noyina ta bayyanawa manema labarai cewa, mijin har yayi aure matarsa na da ciki amma duk da haka bai hakura da maganar tsohuwar matar tasa ba.

Karanta wannan  Batanci: CAN Ta Janye Gabatar Da Zanga-Zangar Da Ta Shirya Kan Kisan Deborah saboda Musulmai ma sunce zasu fito Zanga-Zangar

 

Kamin a gane shine yayi danyen aikin haddashi yaje yiwa tsohuwar matar tasa jaje, matarsa me ciki ce da ta je wajan ta ga galan din fetur din da akace wanda yayi aiki ya bari, tace ai wannan galan dinsu ne.

Tuni dai ‘yansanda sun kama mijin.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.