Dan shekaru 42 a jihar Jigawa, Ibrahim Adamu Mohd ya kashe kansa bayan da wacce yake son aure ta auri wani.
Lamarin ya farune a Kanti dake karamar Hukumar Kazaure ta jihar.
Ranar Lahadi ne dai mutanen yankin suka tashi suka ga gawar Ibrahim a sagale.
Kakakin ‘yansandan jihar, DSP Lawan Shiisu Adam ya tabbatar da faruwar lamarin.
Yace dangin mamacin sun tabbatar da cewa bacin raine yasashi kashe kansa bayan da budurwar tasa ta barshi.