Sojan Najariya me suna Bulama Salish Dake aiki da bataliya ta 232 a karamar hukumar Maiha ta jihar Adamawa ya yiwa yarinya me shekaru 4 fyade.
An kamashi da wannan zargi ne inda aka bayyana sunan mahaifin yarinyar da Mallam Abubakar.
Yanzu dai haka ana kan binciken sojan.
A shekarar 2020 ma dai an kori wani soja daga aiki sannan kuma aka masa daurin shekaru 5 bayan samunsa da laifin fyade a Maiduguri.