An kama wani mutum da ya biya ‘yan daba su kashe mahaifinsa danbya ci gado a jihar Naija.
‘Yansanda sun kama Abubakar Muhammed Buba bayan da ya sa a kashe mahaifin nasa.
Kakakin ‘yansandan jihar, Wasiu Abiodun ya tabbatar da kamen inda yace wanda aka kama din an kamashi ne a kauyen Gidan Madara dake Chanchaga a Minna.
An cakawa mahaifin nasa wuka ne inda ya mutu, amma wanda suka yi aikin sun tsere. Abubakar ya amsa laifinsa.