fbpx
Tuesday, July 5
Shadow

Hoto:Dubu 6 muke karba daga hannun ‘yan Bindigar Zamfara kamin mu yadda su yi lalata damu>>Inji Wadannan ‘yan matan

Wasu ‘yan mata 2, ‘yan uwan juna da aka kama a jihar Zamfara tare da wani dan Achaba da ake zargi yana kaiwa ‘yan bindigar jihar Zamfara kayan Masarufi da matan banza sun amsa cewa Dubu 6 suke karba daga gurin ‘yan bindigar kamin su amince su yi lalata dasu.

 

Hukumar ‘yansandan Civil Defence ta jihar Zamfarace ta kama Shafi’u Abdullahi da ‘yan matan ‘yan uwan juna, Binta Husaini da Balki. An kamasu ne akan hanyarsu ta zuwa karamar hukumar Anka inda acanne suke kaiwa ‘yan Bindigar kayan masarufi.

 

Kwamandan Civil Defence din, Aliyu Garba yace Ranar Juma’ane aka kama mutanen akan hanyarsu bayan da dubunsu ta cika, bayan samun bayanan sirri da aka yi.

Karanta wannan  Bidiyo: Bayan shekara daya, An kama wanda ya kashe Ahmad Gulak

 

Ya kara da cewa, An kamasu ne akan hanyar Bagega zuwa Anka inda dan mashindin din zai kai ‘yan matan 2 masu shekaru 18 da 20 zuwa wajan ubangidansa, dan bindiga me suna Shaho da Abokansa.

 

Abdullahi yace bai taba zuwa maboyar ‘yan bindigar ba, a hanya suke zuwa su karbi koma menene ya kai musu su koma maboyarsu.

 

Hukumar ta Civil Defence ta bayyana cewa da zarar ta kammala bincike zata mikasu zuwa hukuma ta gaba dan daukar matakin da ya dace akansu.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.