Tauraruwar fina-finan Hausa, A’isha Aliyu Tsamiya kenan take karatun kur’ani a kasar Saudiyya inda taje aikin Umrah, ta saka wannan hoton nata a dandalinta na sada zumunta da muhawara inda muatane da dama suka mata fatan Alheri da kuma Allah ya amsa Ibada.
A yayin da da dama suka mata fatan Alheri, wani kuwa cewa yayi ” In Anyi dan Allah ba sai an tallata ba, inko dan a ganine toh mun gani amma ba lada”
Wani kuwa cewa yayi “Sekace gaske”