Matashin soja, Evgeny Stepanovich Kobytev a shekarar 1941 ya tafi yaki wanda aka kammala a shekarar 1945.
Burinsa ya zama kwararre wajan kirkira amma kamin ya cika burin nasa sai kasar Jamus ta kaiwa Soviet union hari wanda hakan ya tursasa masa shiga aikin soja.
Hutudole ya fahimta daga rahoton Vintagenewsdaily cewa sojan ya shekara 4 yana yaki, amma bayan yakin gaba daya kamannin sa sun canja inda ya koma dattijo.
An ajiye hotunan nasa a dakin Tarihi.