Tauraron mawakin Hausa, Ali Isa Jita wanda a baya ya fito zanga-zangar nuna rashin jin dadin kashe-kashen da ake yi a Arewa kuma har aka kai musu hari, ya sake fitowa a yau.
Jita tare da wasu matasa sun fito dauke da kwalaye masu rubutun dake nuna bukatar kawo karshen matsalar tsaro a Arewa.
Ya saka hotunan a shafinsa na sada zumunta kamar haka:
https://www.instagram.com/p/CGc1P_6AWL8/?igshid=1pb8ctecisjr9

