A karon farko, a ranar Alhamis, an ga Shugaba Muhammadu Buhari a cikin jama’a sanye da takunkumin rufe Hanci.
An ga Shugaba Buhari sanye da takunkumin ne a lokacin da ya isa kasar Mali.
Shugaba Buhari na wata ziyarar aiki ta yini guda a Bamako, dake kasar Mali.
