Kasancewar watan Rabi’ul Auwal wata ne da a ka haifi fiyayyan halitta Annabin mu Annabin tsira Annabi Muhammad (S A W).
Hakan ya zamanto lokaci ne da al’ummar musulmai daga sassa daban daban a fadin Duniya ke shirya ta rukan Mauludi domin tunawa da kuma nusar da al’umma kyawawan dabi’u na shugaban Halitta Annabi Muhammad tsira da Amincin Allah su kara tabbata a gareshi da Ahlinsa tare da Sahabbansa.
Itama Masarautar kano ta gudanar da na ta taron Mauludin a fadar Mai martaba Sarkin Kano Aminu Ado Bayero a ranar Alhamis 29 ga watan Oktoban shekarar 2020.
Inda tarun Mauludin ya samu halaratar Mutane daban daban Don tunasar da al’umma girman da Annabi ya ke dashi a wajan Allah Subahanahu wata’ala.