Wani mutum da ya sauka a wani otal a Uyo, jihar Akwa Ibom, an kama shi da Talabijin Plasma da ke dakinsa.
Ya saka Talabijin din a cikin akwatin tafiyarsa kuma ya yi yunkurin tserewa da shi amma an kama shi.
Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne a wani otal da ke Estate Housing Estate, Uyo, kuma an tube shi bayan an gano shi.
Hotunan da suka bayyana a yanar gizo, sun nuna shi a durkushe babu rigar a jikinsa yayin da ya bude akwatinsa yana nuna Talabijin din.
Kamar yadda kuke gani wanda ake zargin yana rokon a masa afuwa yayin da aka bukaci ya rike talbijin na Plasma yayin da ake masa hotuna.