Friday, July 12
Shadow

Hotuna: An kamasu sun sàci mota a masallacin Abuja

‘Yansanda a babban birnin tarayya, Abuja sun kama wasu mutane 2 da ake zargi da satar mota kirar Toyota Corolla.

Kakakin ‘yansandan na Abuja, SP Wasiu Abiodun ya tabbatar da lamarin inda yace an kamasu ne ranar Juma’a.

Yace an kamasu ne a yayin da suke kokarin sayar da Motar a kan Naira Miliyan 6.5 a Minna.

Wadanda aka kama din sune, Gwaza Bulus san kimanin shekaru 41 da kuma Yahya Amodu dan kimanin shekaru 45.

Ana ci gaba da bincike kan lamarin.

Karanta Wannan  DA DUMI-DUMI: Kotu ta haramtawa Aminu Ado Bayero cigaba da bayyana kansa a matsayin Sarkin Kano, ta umurci yan sanda su fitar dashi daga fadar Nasarawa da yake ciki yanzu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *