fbpx
Tuesday, May 24
Shadow

Hotuna: An saka rigar Diego Maradona mai suna ‘Hand of God’ kasuwa akan dala miliyan 5

An saka gwanjon rigar Diego Maradona mai suna ‘Hand of God’ a kasuwa kan kudin naira miliyan 5.

Ita dai wannan rigar itace wadda Diego Maradona ya saka a lokacin da suka fafata da kasar Ingila inda ya zura kwallo a raga da hannu kuma alkalin wasa ya amince da zura kwallon a bisa rashin sani.

Shahararren dan wasan kwallon kafa, wanda ya mutu a shekarar 2020, ya musanya riga da dan wasan tsakiya na Ingila Steve Hodge bayan antashi wasan kusan shekaru 35 da suka gabata.

Karanta wannan  Kalli Bidiyon kayatacciyar kwallon da Balotelli yaci data dauki hankula

Yanzu Hodge ya sanya rigar kasuwa don siyarwa a Sotheby’s kuma an fara tallarta.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.