fbpx
Tuesday, July 5
Shadow

Hotuna: An shakewa wani barawon wayoyin wutar lantarki kwano da taliya kafin a masa dan banzan duka a Bayelsa

An shakewa wani barawon wayoyin wutar lantarki kwano da taliya kafin a kara masa dan banzan duka a unguwar Agorogbene, karamar hukumar Sagbama ta jihar Bayelsa.

Wanda ake zargin mai suna Preye Ayase da wani abokinsa, Ringo Tareladei, an kama su dumu-dumu a daidai lokacin da suke lalata igiyoyin wutar lantarki da ke hade yankin Ogobiri da Agorogbene a cikin Sagbama a ranar Laraba, 20 ga Afrilu.

A halin da ake ciki, Ouseibai Seperegha Godsgift M, shugaban kungiyar Creek Youths Agenda (CYA) yayi Allah wadai da sata da lalata igiyoyin lantarki (kebul) da suka haɗa al’ummomin biyu.

A wata sanarwa da babban sakataren yada labaran sa Mista Ebis Okpeke ya raba wa manema labarai ya bayyana cewa shugaban kungiyar ya nuna rashin jin dadinsa da faruwar lamarin inda ya yi kira ga matasan yankin da su kaurace wa irin wannan aika-aikar ba tare da bata lokaci ba domin hakan ba zai haifar masu da da mai ido ba.

Karanta wannan  Yan sanda sun kama wasu mutane 7 da ake zargin 'yan kungiyar asiri ne tare da kwato makamai a Jihar Edo

Shugaban na CYA ya kuma yi amfani da wannan dama wajen yin kira ga gwamnatin jihar Bayelsa da ta kawo agaji ga al’ummar da abin ya shafa wajen dawo da wutar lantarki.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.