Tsohon Mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana kaiwa mahaifiyar tsohon shugaban kasa, marigayi Alhaji Umar Musa ‘Yaradua ziyara a Katsina.
Atiku yace ziyarar da ya kai Katsina ba zata kammalu ba idan bai kaiwa Hajiya Aya Dada ‘Yaradua ziyara ba.
Yace ta masa addu’ar fatan Alheri da kuma samun zaman Lafiya a Najeriya.
I’m happy to have met her in good condition. She prayed for my success and peace and unity to return to our dear country. -AA
— Atiku Abubakar (@atiku) May 18, 2022
