Gidauniyar me kamfanin BUA, Abdulsamad Rabiu watau BUA Foundation ta baiwa jihar Katsina tallafin motocin daukar mara lafiya 3.
BUA ya bada tallafin motocinne dan ci gaba da yaki da cutar Coronavirus/COVID-19 a jihar.
Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari ne ya bayyana haka ta shafinsa na Twitter, kamar yanda hutudole ya samo.

Ya yabawa BUA da wannan kokari inda yace Allah ya saka masa da Alheri.
Saidai yayi amfani da wannan dama inda ya roki BUA din ya tallafa musu a kan ginin gurin killace masu cutar Coronavirus/COVID-19 da jihar ke yi me daukar gadaje 700.
What you have been doing in this line across the nation is really most commendable.
May I use this opportunity to seek for more support from you in the area of equipping a 700 bed capacity isolation center we are working on. May Allah reward you abundantly. pic.twitter.com/Rh1XYX41yI
— Aminu Bello Masari (@GovernorMasari) May 28, 2020
A baya dai BUA ya bayar da tallafi me kwari sosai dan tallafawa yaki da cutar Coronavirus/COVID-19 a matakin gwamnatin tarayya dana jihohi.