fbpx
Thursday, August 18
Shadow

Hotuna: Cristiano Ronaldo ya je kallon wasan El clasico kuma ya nuna farin ciki sosai da nasarar Real Madrid

Gwarzon dan wasa  Kuma mai taka leda a Juventus Cristiano Ronaldo ya yi amfani da lokacin hutu a gasar Italiyan Serie A, saboda tsoron Coronavirus da ta bulla a kasar Italia, inda dan wasan ya kasance a filin Santiago Bernabeu don kallan  karawar da kungiyar Real Madrid ta El Clasico da ta yi da Barcelona a ranar Lahadi.
Dan wasan mai shekaru 35 ya shiga filin wasan ne cikin sirri  don gudun kada wasu masoya su gano shi, hakan ya  nuna cewa har yanzu kulob din madrid yana nan aransa, bayan da aka nuna shi yana murnar Nasarar da tsohuwar kungiyarsa ta samu lokacin da vinicius jrs ya zura kwallo, a inda madrid ta doke 2-0. Barcelona
Vinicius ne ya fara zura kwallo, a minti na 71 har ma ya kwaikwayi shahararren dan wasan Ronaldo, Inda aka nuna shi yana yabawa ga dan wasan.
 Wannan shi ne karo na farko da Ronaldo ya dawo kungiyar.
Nasarar da ta yi a daren ya tabbatar da cewa Madrid ta koma saman teburin La liga.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Karanta wannan  Manchester United zata dauki Casemiro daga Real Madrid

Leave a Reply

Your email address will not be published.