Wasu matasan Arewa a jihohi da yawa sun fito Zanga-Zangar nuna rashin jin dadi kan matsalar tsaron da ta mamaye jihohin Arewa.
Zanga-Zangar ta faru ne a jihohin Bauchi, Zamfara, Zamfara, Kano da Sokoto.
Hakanan an yi Zanga-Zangar a babban birnin tarayya Abuja.
Wadda ta jagoranci Zanga-Zangar a Kano, Zainab Nasir Ahmad ta ce an gaji da kashe jama’a kullun dan haka suke aika sako ga gwamnati ta dauki mataku.